14 Nuwamba 2020 - 11:09
Libya: An Sanya Ranar 24 Ga Watan Decemban Shekara Ta 2021 A Matayin Ranar Zaben Shugaban Kasa

Libya: An Sanya Ranar 24 Ga Watan Decemban Shekara Ta 2021 A Matayin Ranar Zaben Shugaban Kasa tattaunawa tsakanin yan kasar Libya ya tsaida cewa za’a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar a ranar 24 ga watan Decemba na shekara ta 2021 mai kamawa.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto jakadan majalisar dinkin duniya na musamman kuma na riko a kasar ta Libya yana fadar haka a jiya Jumma a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia inda ake taron.

Stephanie Williams ya kara da cewa akwai bukatar a sami sabbin shuwagabanni wadanda zasu sake hada kan mutanen kasar sannan su gabatar da sauye-sauyen a bangarori da dama a kasar don fitar da kasar daga mumunann halin da take ciki.

A watan da ya gabata ne dai aka tsagaita budewa juna wuta tsakanin sojojin Halifa Haftar na gabacin kasar da kuma na Fa’iz Sarraj wanda yake iko da Tripoli.

Tun shekara 2011 ne, bayan kifar da gwamnatin Kaddafi Libya da fada cikin yakin cikin gida.

342/